Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{A.S} - ABNA : ya nakalto KhadibZade yana maida martini ga labaran da suke fitowa daga bangaren tsohon shugaban kasar ta Yemen Abdu Rabbu Mansur Hadi wadanda suke cewa sun kashe wani ba’irani a fafatawarsu da sojojin kasar..
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya kara da cewa Iran bata taba turawa sojojin Yemen mai bada shawara kan harkokin tsaro ba, tun farkon yakin a shekara ta 2015 har zuwa yanzu.
Ya ce: Amma sau da dama Saudia da kawayenta wadanda suke kashe mutanen Yemen tare da taimakon wasu lalatattun yan kasar, suna cewa kasar Iran ce take jujjuya yakin na kasar ta Yemen.
Tun cikin watan Maris na shekara ta 2015 ne kasar saudia da wasu kawayenta na kasashen Larabawa suka farwa kasar Yemen da yaki, da nufin maida tsohon shugaban kasar Abdu Rabbu Mansur Hadi kan kujerar shugabancin kasar.
342/