Matasan da suka fito kan tutuna a Accra babban birnin kasar ranar Laraba, na rika daga kwalaye da aka yiwa rubutu da ke cewa "Cin hanci na haifar da talauci" wasu kuma na cewa "A gyara tsarin Ilmin mu a yanzu"
Zanga zangar ita ce ta baya bayan nan tun watan Maris a jerin zanga zangar adawa da gwamnati bayan da kotun kolin kasar ta yi watsi da karar da yan adawa suka shigar na kalubalantar nasarar sake zabar Akufo-Addo a bara.
Tun bayan sake zabensa, shugaba Nana Akufo-Addo na fuskantar matsin lamba yayin da kasar ta yammacin Afirka ta fada matsalolin tattalin arziki wanda ya kara tabarbarewa sakamakon annobar korona.
Masu zangar zangar dai na bukatar a samar da gyara dangane da yadda ake tafiyar mulkin kasar.