16 Afirilu 2021 - 13:35
Iran Za Ta Iya Tace Sanadarin Urani’um Da Daraja 90%, Amma Ba Ta Nufin Kere Bom

Shugaban kasar Iran Dr. Hassan Rauhani ne ya bayyana cewa; Za Mu Iya tace sanadarin urani’un da darajar da za ta kai 90%, amma ba manufarmu ce mu kera bom din Nukiliya ba.

ABNA24 : Shugaban kasar ta Iran wanda ya bude wasu manyan ayyuka guda hudu na tantance dangogin man fetu (petrochemical) a yau Alhamis ta hanyar bidiyo daga nesa, ya kuma yi watsi da damuwar da Amukra da kasashen turai uku su ka nuna saboda yadda Iran din ta kai darajar urani’um din da take tacewa zuwa 60%.

Shugaban na kasar Iran ya zarge su da cewa su ne su ka ja Iran din take daukar matakan da take dauka a wannan lokacin, amma da zarar sun koma kan aiki da yarjejeniyar, to Iran din za dakatar da tace Uranium da daraja 20% da kuma 60%.

342/