ABNA24 : Gwamnan ya kara da cewa ya zuwa yan an kawo jami
An tsaro na musamman 100 dawo da zaman lafiya a jihar sannan ana saran yawansu zai kai 250 a cikin ‘yan kwanaki masu zuwa.
A makon da ya gabata ne ‘yan sanda suka kashe wani bakin fata a garin Kenosha na jihar ba tare da yana dauke da makami ba a gaban ‘yayansa. Wannan kissan ne ya tada borin da ya fi karfin jami’an tsaron jihar, har saida ta nemo tallafi daga gwamnatin tarayyar kasar.
Tsarin yadda ‘yan sandan Amurka suke bi wajen kisan bakaken fata akasar dai yana tabbatar da bambamcin launin fara a fila. Wanda ya kai ga al-ummar bakaken fatar kasar da kuma masu goyon bayansu suke bukatar a sauya tsarin.
342/