6 Agusta 2020 - 12:17
Iran : Jagora Ya Jajantawa Al'ummar Lebanon Bayan Fashewar Data Auku

Jagoran juyin juya halin musulinci na Iran, ya isar da sakon ta’aziyya da jaje ga al’umma da gwamnatin Lebanon, biyo bayan mummunar fashewar data auku a kasar a ranar Talata data gabata.

ABNA24 : A sakonsa na twitter, Ayatollah Sayyid Ali Khamne’I, ya ce muna jajantawa al’ummar kasar Lebanon, kuma muna goyan bayansu a wannan lokaci bayan fashe fashen da suka auku a tashar ruwa ta Beirut, wacce ta haddasa hasara ta rayuka da dukiyoyi a wannan kasa ta Lebanon.

Jagoran ya kuma ce hakuri a daidai wannan lokaci, shi ne abu mafi dacewa ga kasar ta Lebanon.

Dama kafin hakan manyan jami’an kasar ta Iran da suka hada da shugaban kasar, da na majalisar dokoki da kuma ministan harkoin waje, sun aike da irin wannan sakon na ta’aziyya da jaje ga kasar ta Lebanon.

Kawo yanzu dai a cewar hukumomin kiwon Lafiya na Lebanon mutum 135 ne suka rasa rayukansu a fashewar tare da jikkata wasu 5,000 sai kuma wasu sama da 300,000 da suka rasa muhallensu.

Har yanzu kuma akwai adadin mutanen da ba a san inda suke ba.

Tuni dai kasashen duniya, suka fara kai dauki wa kasar ta Lebanon ta hanyar kai magunguna da ababen bukatuwa na yau da kulun.

342/