3 Mayu 2020 - 04:57
 Sayyid Hassan Nasrallah Ya Yi Wa Ma’aikata Murnar Zagayowar Ranarsu Ta Duniya

Sayyid Nasrallah wanda ya gabatar da jawabi a ranar ‘yan kwadago ta duniya a jiya Juma’a, ya bayyana cewa; Muna yin jinjina da girmamawa ga dukkanin ‘yan kwadago.

(ABNA24.com) Sayyid Nasrallah wanda ya gabatar da jawabi a ranar ‘yan kwadago ta duniya a jiya Juma’a, ya bayyana cewa; Muna yin jinjina da girmamawa ga dukkanin ‘yan kwadago.

Jagoran na kungiyar ta Hizbullah a kasar Lebanon, ya kuma yi bayani akan watan Ramadhan mai alfarma, inda ya ambaci falalarsa wanda ya ce yana kunshe ne da hakuri da abin yabo ne da Allah ya yi wa muminai da masu jihadi.

Sayyid Nasarallah ya kara da cewa; Idan muna son zama abin kauna ga Allah, to wajibi ne a gare mu, mu zama masu hakuri, domin Allah yana son masu hakuri.

Jagoran na kungiyar Hizabullah ya kara da cewa; Matsayi mafi girma shi ne mutum ya sami yakini da cewa Allah madaukakin sarki yana a tare da shi a kodayaushe.



/129