(ABNA24.com) Inna Lillahi Wa Inna Ilaihi RajiunAllah ya yiwa babban malamin addinin musuluncin nan na Jamhuriyar Musulunci Ta Iran dake zaune a birnin Qum mai tsarki Ayatullah Ibrahim Amini rasuwa a daren Jummu’ar nan data gabata.
Ayatullah Amini ya rasu ne bayan wata jinya da yayi a babban asibitin DR Beheshti dake birnin na Qum.
Ya kasance cikin manyan malamai dake da hannu wajen rike Jamhuriyar Musulunci kuma ya zama mamba a majalisu manya na kasar.
Muna masu mika jaje da ta’aziyyar wannan babban rashi ga Sahibul Asr [AF], Sayyid Qa’id, da sauran al’ummar musulmi baki daya.
/129
2 Mayu 2020 - 03:42
Lambar labari: 1032223
Inna Lillahi Wa Inna Ilaihi RajiunAllah ya yiwa babban malamin addinin musuluncin nan na Jamhuriyar Musulunci Ta Iran dake zaune a birnin Qum mai tsarki Ayatullah Ibrahim Amini rasuwa a daren Jummu’ar nan data gabata.