24 Satumba 2026 - 22:35
Source: ABNA24
Najeriya: Ana Cigaba Da Yi Wa Sheikh Yakub Yahya Ta'aziyyar Rasuwar Sheikh Ammar + Hotuna

A jiya Laraba 23/09/2026, aka shiga rana ta uku da fara gudanar da zaman ta’aziyyar Sheikh Ammar, wadda Sheikh Yakub Yahya Katsina, ke jagoranta a gidan shi da ke Kofar Kaura, Katsina.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Bayt (AS) – ABNA – ya ruwaito cewa: Al’umma da dama su na cigaba da yi wa Sheikh Yakub Yahya gaisuwa, waɗanda suka haɗa da Tawagar ’yan uwa daga da’irar Zariya, wadda ta samu wakilci Sheikh Abdulhamid Bello, Frofesa Abdullahi Danladi, Frosefa Meshalgaru, sannan akwai tawaga ta musamman daga fadar Sarkin Katsina, Alhaji Dr. Abdulmuminu Kabir Usman, akwai kuma shugaban karamar hukumar Katsina, Hon. Isah Miqdad, tawagar wasu ba’alin ’yan uwa daga da’irar Kano, ’yan uwa na Imam Ridah Family Abuja, da sauransu.

Har wala yau, a cikin masu ziyarar akwai, Wazirin Katsina, Alhaji Ibrahim Ida, wakilin magajin garin Katsina, kuma limamin Shinkafi, Alhaji Abdu Iliyasu, Alkalin Kotun Musulunci ta Kofar Soro, Alkali Ƙasimu, Khadimul Qur’an Alhaji Abdun Malam, ’yan uwa na Dandali Matasa na kasa baki daya, Alhaji Ibrahim Falala, Tawagar Sheikh Nasir na Malam Sidi, ɗaki tara, Malam Abdulkadir Khalifan Shehu Namadi, da sauransu.

Haka kuma, a cikin masu ziyarar akwai, wakilai daga kamfanin Green House Katsina, da kuma Ambassada Aminu Yusuf Mamandi, daga Human Right, tawagar sha’irai ta jihar Katsina, karkashin jagorancin Malam Shafi’u Mai Inyass, tawagar Uzairiyya Group ta yankin Katsina, wakilin ’yan uwa na da’irar Malumfashi, Malam Kabir Imam, wasu ba’alin ’yan uwa na yankin Batsari, tsaffin ɗaliban Makarantar Tahfizul Qur’an Katsina, Malam Iyal Gafai, da sauransu.

24.Sept.2026

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha