(ABNA24.com) Babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sayyid Hassan Nasrullah ya bayyana yaki da cutar corona a matsayin aiki ne na ‘yan adamtaka zalla.
A lokacin da yake gabatar da wani jawabi a daren jiya wanda kafofin yada labarai na ciki da wajen kasar Lebanon suka watsa kai tsaye, babban sakataren kungiyar Hizbullah Sayyid Hassan Nasrullah, ya yi ishara da wajabcin hada karfi tsakanin al’ummomin duniya domin yaki da cutar corona.
Ya ce nauyi na farko ya rataya ne kan hukumomi da cibiyoyin kiwon lafiya na duniya da kuma na daidaikun kasashe, kamar yadda kuma masu hannu da shuni za su iya taimaka wa da duk abin za su iya domin gudanar da wannan aiki na ‘yan adamtaka.
Dangane da sauran jama’a kuwa, Sayyid nasrullah ya bayyana cewa, mataki na farko na fuskantar lamarin shi ne dogaro ga Allah, da kuma kaskantar da kai a agare shi da rokonsa kariya, sannan kuma a kiyaye dukkanin abubuwan da masana da cibiyoyin kiwon lafya suke fada dangane da lamarin da kuma yadda za a kare kai.
Nayyid Nasrullah ya bayyana shugaban kasar Amurka Donald a matsayin babban makaryaci, dangane da yadda ya yi ta shirga wa duniya karya kan batun cutar ta corona, da kuma yadda yake nuna cewa lamarin ba zai taba shafar Amurka da Burtaniya ba sakamakon matakan da suka dauka.
Dangane da hare-haren da Amurka ta kaddamar jiya Juma’a akan sansanonin sojin kasar Iraki kuwa, ya bayyana hakan da cewa abin Allawadai dai, tare da tabbatar da cewa Amurka ce take kara kusanto da lokacin ficewar daga kasar Iraki da kanta.
/129
15 Maris 2020 - 07:06
Lambar labari: 1017546
Babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sayyid Hassan Nasrullah ya bayyana yaki da cutar corona a matsayin aiki ne na ‘yan adamtaka zalla.