-
Majiyar Tsaron Lebanon: An Sanya Bama-Bamai Ne Cikin Na’urorin
Adadin Wadanda Suka Jikkata A Lamarin Yau A Kasar Labanon Ya Kai Dubu 4, Yayin Da Adadin Shahidai Ya Kai 11.
-
Bidiyoyin Irin Ta’adin Da Harin Da Isra’ila Ta Kai Lebnon Ya Haifar
Wata Majiyar Tsaro Ta Shaidawa Aljazeera Cewa Fashewar Na'urorin Sadarwa A Kasar Lebanon Ya Faru Ne Sakamakon Kutse Ta Hanyar Amfani Da Fasahar Mara Waya. Rahotanni sun nuna cewa wannan fashe-fashe bai takaita da Dahiya kadai ba, a’a ya faru a duk fadin kasar Lebanon, kuma a lokaci guda wasu wayoyi, wayoyin hannu da bututun waya sun fashe.
-
Fashewar Na’urorin Hizbullah A Fadin Kasar Lebanon/ Fiye Da 'Yan Lebanon 1,000 Ne Suka Jikkata Sakamakon Fashewar Na'urorin Pager.
Gwamnatin yahudawan sahyoniya ta fasa na’urorin dakarun Hizbullah na kasar Labanon.
-
Hukumar Leken Asirin Ta Taliban Ta Gargadi 'Yan Shi'a Da Ke Yammacin Kabul Da Su Guji Taruwa Saboda Barazanar Ta'addancin ISIS
Hukumar leken asiri ta Taliban ta sanar da hukumar kula da harkokin tsaro ta mabiya mazhabar Shi'a cewa, wasu daga cikin 'yan kungiyar ta'addanci ta Da'esh suna da wanzuwa a yammacin birnin Kabul.
-
Labarai Cikin Hotuna Na Yadda Aka Yi Jana'izar Shahidan Daikundi Afganistan
Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul-Baiti As - ABNA ya ya habarta cewa: an gudanar da jana'iza da bankwana na shahidan da kungiyar ta'addanci ta Da'ish ta kai wa 'yan shi'ar kauyen "Qariyudal" da ke lardin Daikundi na kasar Afganistan tare da haartar dimbin jama'a.
-
Dukkan Mutanen Kauyen “Garyudal” Da Ke Daikundi Sun Yi Shahada A Harin ISIS Suka Kai Afganistan
Ya kalli gidajen kauye sannan ya kalli gawarwakin shahidan. Yana so ya ce in ban da mu maza uku, babu wani mutum da ya tsira a wannan karamin kauye.
-
Martanoni Masu Yara Dangane Da Kisan Kiyashin Da Ake Yi Wa 'Yan Shi'ar Daikundi Afghanistan
Bayan harin ta'addancin da aka kai kan 'yan Shi'ar Daikundi na kasar Afganistan, wanda ya yi sanadin shahadar mutane 14, mutane da kungiyoyi da dama na kasar Afganistan sun mayar da martani da dama suna masu nuna Allah wadai din su akan haka.
-
Yaman Ta Kai Hari Tel Aviv Da Makami Mai Linzami Na Ultrasonic ballistic / A Tsawon Kilomita 2,400 Cikin Kasa Da Mintuna 12.
Kakakin Rundunar Sojin Yaman: Zamu Sanya Makiya Suyi Nadamar Ranar Da Suka Kawo Mana Hari
-
Kungiyar Hizbullah Ta Sake Yi Ruwan Makamai Masu Linzami Kan Gwamnatin Sahyoniyawa
Majiyoyin labarai sun ba da rahoton cewa, an harba rokoki da dama a cikin yankunan da aka mamaye tare da kara kararrawa a yankuna daban-daban na sahyoniyawa.
-
'Yan Ta'addan Daesh Sun Kai Wani Mummunan Akan Mabiya Mazhabar Shi'a A Afganistan Fiye Da Mutum Gom Ne Suka Mutu
Sama da fararen hula 10 ne suka mutu a wani harin ta'addanci da kungiyar Daesh ta kai a kasar Afganistan a daidai lokacin da suke taruwa domin tarbar maniyyata da suka taho daga wurare masu tsarki a Karbala.
-
Husain Tavakoli Ya Saki Sabon Wake Mai Taken "Palestine Azadbad" Don Nuna Goyon Bayan Falasdinu Da Gaza
Gajeruwar waka mai taken "Free Free Palestine!" An yi ta ne a matsayin waƙar zanga-zangar nuna goyon baya ga al'ummar Palastinu da Gaza. Wannan aikin waka yana wakiltar muryar gwagwarmaya da masu neman 'yanci a duniya don kawo karshen ‘yan mamaya da zalunci a cikin Falasdinu. Hussain Tavakoli ne ya rubuta tare da rera wannan waƙa kuma tarin yaruka na duniya wanda suke rerawa a taken da aka ji a jerin gwanon goyon bayan Falasɗinu ne a gabaki dayan duniya.
-
Kungiyar Kare Hakkin Bil Adama: Gwamnatin Sahyoniyawa Tayi Amfani Da Na’urar AI Wajen Kisan Gillah A Gaza
An Samu Shahidai 60 Da Jikkata 40 A Harin Da Sojojin Yahudawan Sahyoniya Suka Kai A Kan Tantin 'Yan Gudun Hijira A Birnin Khan Yunus.
Kungiyar kare hakkin bil adama ta bayyana damuwarta game da yadda gwamnatin sahyoniyawa ta yi amfani da Na’urar AI na wucin gadi wajen kisan kiyashi a Gaza da kuma sakamakon da zai haifar a dabi'ance da shari'a.
-
Labarai Cikin Hotuna Na Karancin Ruwan Sha A Khan Yunis
Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul-Baiti As - ABNA ya bayar da rahoton cewa: bayan ci gaba da hare-haren da sojojin yahudawan sahyuniya suke kaiwa a yankuna daban-daban na Gaza, da wuya ake samu ruwan sha mai tsafta a birnin Khan Yunus, wanda ya zamo Palasdinawa mazauna wannan birnin dole sai sun dauki sa'o'i akan layi a kowace rana don samun ruwan tsaft
-
An Nemi A Gurfanar Da Wadanda Suka Aikata Laifukan Lalata Da Fursunonin Falasdinu
Bramila Batten, wakiliyar babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya ta musamman kan cin zarafin mata a lokutan yaki da tashe-tashen hankula, ta bayyana damuwarta dangane da rahotannin baya-bayan nan da wannan kungiya ta fitar game da mummunar tabarbarewar yanayin fursunonin da ake tsare da su a gidajen yarin yahudawan sahyoniya.
-
Shugaban Kungiyar Malaman Pakistan: Magoya Bayan Sahyoniyawa Ba Su Da Wurin Zama A Pakistan
Shugaban kungiyar Malaman Pakistan ya ce: Tabbas a yau duniya ta gane cewa al'ummar Pakistan sun rufe batun daidaitawa da sulhu da Isra'ila, kuma babu wani wuri a Pakistan ga magoya bayan sahyoniyawan da masu neman daidaitawa da haramtacciyar kasar Isra'ila.
-
Mawallafar Majalisar Ahlul Baiti (AS) Ta Samu Halartar Wajen Baje Kolin Littafai Na Kasa Da Kasa Karo Na 25 Na Bagadaza.
Wallafe-wallafen Majalisar Ahlul-Baiti (AS) za su halarci taron baje kolin littafai na kasa da kasa karo na 25 a birnin Bagadaza.
-
Labarai Cikin Hotuna Na Kawata Birnin Sana'a Da Koren Kal A Jajiberin Maulidin Manzon Allah (SAW)
Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul-Baiti As - ABNA - ya habarta cewa: al’ummar kasar Yemen a birnin San’a da wasu lardunan kasar na shirin gudanar da bukukuwan maulidin manzon Allah (SAW) ta hanyar fente motocinsu da kore, tare da yin ado da kayan ado da sanyawa tituna korayen tutoci da fitulu. San’a ta bunkasa da jerin gwanon daruruwan motoci da aka yi wa ado da take masu haske da kore domin murnar zagayowar ranar haihuwar Manzon Allah (SAW).
-
Yaman Ta Harbo Wani Jirgi Mara Matuki Kirar MQ 9 Na Sojojin Amurka
Kakakin Rundunar Sojin Yaman ya sanar da cewa: Dakarun tsaron saman kasar sun yi nasarar harbo wani jirgin yakin Amurka mara matuki mai suna "MQ 9" a lokacin da suke gudanar da ayyukan daga a sararin samaniyar lardin Marib.
-
Wata Yarinya Ta Yi Shahada Sakamakon Harbin Da Sojojin Mamaya Suka Yi Mata A Garin Qaryut
Wata yarinya mai suna Bana Amjad Bakr (mai shekaru 13) ta yi shahada sakamakon harbin bindiga da sojojin mamaya suka yi mata a kirji, a yammacin yau Juma'a, bayan wani hari da 'yan mulkin mallakan sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila suka kai musu a kauyen Qaryut da ke kudancin Nablus.
-
Hukumomin Isra'ila Sun Yi Gargadi Game Da Mayar Da Yammacin Kogin Jordan Zuwa Gaza Ta Biyu
Tare da karuwar alamun wanzuwar wani gagarumin shiri na mayar da yammacin kogin Jordan zuwa wani nau'i na biyu na zirin Gaza, ta fuskar rusau, kora, kisa, kamawa, da cin zarafi,... tare da harin Isra'ila a kan garuruwa da sansanonin Yammacin Kogin Jordan, kuma nan ba da jimawa ba zai juya zuwa "fuskoki biyu," inda da gajeren makamai masu linzami, irin su Katyushas da sauransu na iya zama makaman da za’a iya kai harin bam a Tel Aviv.
-
Jordan: Ta Yi Kira Da A Haramta Sayar Da Makamai Ga Isra'ila
Ministan harkokin wajen kasar Jordan yayin da yake goyon bayan matakin da Birtaniyya ta dauka na dakatar da lasisin aika nau'ikan makamai iri 30 ga gwamnatin sahyoniyawa, ya bukaci dukkanin kasashen duniya da su hana sayar da makaman soji zuwa wannan gwamnatin.
-
Al-Qassam Ta Wallafa Faifan Bidiyon Wanda Aka Yi Garkuwa Da Shi Na Karshe Daga Cikin Mutane Shida Da Aka Kashe Fursunonin Sahyoniyawan
Bataliyar shahidi Ezzuddin Al-Qassam reshen soja na Hamas ta fitar da wani faifan bidiyo na fursinoni na karshe na gungun fursinonin yahudawan sahyoniya 6 wadanda a baya-bayan nan gwamnatin sahyoniyawa ta yi ikirarin dawo da gawarwakinsu daga Gaza.
-
Hizbullah Ta Kai Hare-Hare Kan Barikin "Ramut Naftali" Na Sojojin Yahudawa
Hare-haren da mayakan Hizbullah suka kai a barikin "Ramut Naftali" na sojojin yahudawan sahyoniya ya kara tsanani.
-
Shugaban Kungiyar Ansarullah Ta Yaman: Laifukan Dabbanci Na Isra'ila Ya Kai Ga Cutar Da Zukatan Wadanda Ba Musulmi Ba.
Musulman Gaza na fama da munanan hare-hare da kashe-kashen gilla da Isra'ila ke yi, wanda ke cutar da al'ummomin kasashen da ba musulmi ba.
-
An Kama Wasu Matasa 4 'Yan Kasar Bahrain Bayan Da Suka Halarci Tattakin Arbaeen Husaini As
Jami'an tsaron gwamnatin Al-Khalifa sun kama wasu matasa 'yan kasar Bahrain guda hudu wadanda suka halarci tattakin Arbaeen din Imam Husaini As ba tare da wani dalili na shari'a ba!
-
An Kai Wa Ayarin Motocin Gwamnan Birnin Daraa Na Kasar Syria Hari
A cikin wata sanarwa da ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar ta Siriya ta fitar ta sanar da harin ta'addanci da aka kai kan ayarin motocin gwamnan Daraa a kudancin kasar ta Siriya.
-
Dakarun Islama Na Iraqi Sun Kai Hari Kan Tashar Jiragen Ruwan Haifa A Yankin Falasdinu Da Aka Mamaye
An kai hari tashar jiragen ruwa ta Haifa da wasu jirage marasa matuki.
-
Hamas Ta Ɗauki Sabbin Sojoji 3,000
Tashar talabijin ta sahyoniya ta 12 ta sanar da cewa bayan fiye da watanni 10 da fara yakin, kungiyar Hamas ta yi nasarar sake gina karfinta a arewacin zirin Gaza.
-
Rahoto Cikin Hotuna Na gudanar da zaman makokin wafatin Annabi Muhammad (SAW) a birnin Kargil na kasar Indiya
Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul-Baiti As - ABNA - ya kawo maku rahoton cewa: an gudanar da zaman makoki na zagayowar ranar wafatin fiyayyen halitta Annabi Muhammad (SAW) a birnin Kargil na kasar Indiya, tare da halartar dinibin masoya Ahlulbaiti (A.S.).
-
Labarai Cikin Hotuna Na Zaman Makoki Akwanaki Goma Na Karshen Watan Safar A Kauyen "Bajgah" Da Ke Birnin Balkhab Na Kasar Afganistan.
Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul-Bait (a.s) ya habarto maku cewa: an gudanar da zaman makoki a cikin kwanaki goma na karshen watan Safar a kauyen "Bajgah" da ke birnin Balkhab na kasar Afganistan. A cikin wannan taron na Hujjatul-Islam wa Muslimin, Sayyid Haidar Hashimi, limamin 'yan Shi'a na Juma'a a Mazar-e-Sharif ne ya gabatar da jawabi.