Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul-Baiti
As - ABNA ya habarta cewa: majiyoyin yada labarai sun bayar da rahoton faruwar
wani lamari na tsaro ga dakarun Hizbullah na kasar Labanon a yankuna daban-daban
na wannan kasa tare da yunkurin kashe wasu daga cikin wadannan dakarun.
Bisa labarin da aka bayar, an ce gwamnatin yahudawan sahyoniya ta yi nasarar kutsa kai cikin na'urorin sojojin Hizbullah tare da tayar da wadannan na'urori.
Majiyoyin cikin gida sun sanar da cewa sama da sojojin Hizbullah dubu ne suka jikkata sakamakon wadannan fashe-fashe kuma an kai su asibitoci daban-daban na kasar Labanon domin yi musu magani.
Har ila yau, wani yaro da mayakan Hizbullah biyu sun yi shahada a wadannan fashe-fashe.
Ma'aikatar lafiya ta Lebanon ta bukaci duk 'yan kasar da ke da da wanna na’ura da da su nisanta da ita har sai hakikanin abun yaa bayyana.
Dangane da haka, wani tsohon jami'in na Shabak ya yi ikirarin cewa: Fashewar na'urorin pager na daruruwan dakarun Hizbullah wani aikin kutse ne da ba a taba yin irinsa ba.
Tashar talabijin ta 12 ta gwamnatin Sahayoniyya ta kuma bayyana cewa, fitaccen mashawarcin Netanyahu a fakaice ya tabbatar da hannun Isra'ila a fashewar wadannan na'urori.
Sauran rahotannin na nan zuwa yayin da aka kamala da tabbatarwa….