Wata yarinya mai suna Bana Amjad Bakr (mai shekaru 13)
ta yi shahada sakamakon harbin bindiga da sojojin mamaya suka yi mata a kirji,
a yammacin yau Juma'a, bayan wani hari da 'yan mulkin mallakan sojojin
haramtacciyar kasar Isra'ila suka kai musu a kauyen Qaryut da ke kudancin
Nablus.
Kungiyar agaji ta Red Crescent ta Falasdinu ta bayar da rahoton cewa, ma’aikatanta sun yi duba da wata yarinya da ta samu munanan raunuka sakamakon harsasai masu rai da aka harbeta a kirji, a lokacin arangamar da ta barke tsakanin sojojin mamaya a yankin Qaryut, kuma an dauke ta zuwa asibitin tiyata na gwamnatin Rafidiya da ke Nablus, inda likitocin suka ta bayyana shahadarta a sakamakon raunin da ta samu.
Mahaifin Shahidiyar ta fada cewa, ‘yarta ta samu harbin bindiga daga sojojin mamaya a lokacin da take cikin dakinta da ke gida tare da ‘yan uwanta mata.
Tun da farko, wani matashi (mai shekaru 34) ya samu raunuka sakamakon harbin da aka harba a hannunsa, sannan wani (mai shekaru 30) ya samu raunuka bayan wasu ‘yan mamayar suka kai musu hari a kauyen.
Majiyoyin cikin gida sun ruwaito cewa wasu sojojin ‘yan mamaya sun kai farmaki a garin Qaryut, inda suka kai hari gidajen ‘yan kasar a kudancin kauyen, tare da dukansu.
Majiyar ta kara da cewa sojojin sun kona filaye a kauyen.
Tare daa da shahadar wanna yarinyar, adadin shahidai a yammacin kogin Jordan tun daga ranar bakwai ga watan Oktoban da ya gabata ya kai shahidai 692, ciki har da kananan yara 159, Baya ga hadin kan Amurka ga wanna ta’addanci a cewar bayanan ma'aikatar lafiya.