9 Satumba 2024 - 10:07
Mawallafar Majalisar Ahlul Baiti (AS) Ta Samu Halartar Wajen Baje Kolin Littafai Na Kasa Da Kasa Karo Na 25 Na Bagadaza.

Wallafe-wallafen Majalisar Ahlul-Baiti (AS) za su halarci taron baje kolin littafai na kasa da kasa karo na 25 a birnin Bagadaza.

Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul-Baiti As - ABNA - ya habarta cewa: shafin yada labarai na majalisar Ahlul-Bait (AS) zai halarci bikin baje kolin litattafai karo na 25 na birnin Bagadaza.

 "Mustafa Behbahanipour", Darakta Janar na Hidima da Wallafa na Majalisar Ahlul Baiti (AS) ta duniya ne ya sanar da wadannan labaran da ke sama, ya kuma kara da cewa: Kamfanin Wallafar Majalisar Ahlul Baiti (AS) ta duniya da nufin musayar ra'ayi da fadada sadarwa da kuma Mu'amala da mawallafan Iraki da mawallafofin ƙasashen Larabawa, zata halarci taron baje-kolin litattafai karo 25 a Bagadaza, wanda za a fara daga ranar 12 ga Satumba kuma za’a ci gaba da gudanar da shi har zuwa 22 ga Satumb.

Ya kara da cewa: bayyanar da sunayen littafai 64 na rubuce-rubucen Majalisar, gabatar da aikace-aikacen Naba a cikin harsuna da dama, tantancewa da kuma bin diddigin ayyukan buga littattafai a kasashen Larabawa da Iraki, na daga cikin sauran manufofin halartar wannan taron.

Behbahanipour ya yi nuni da cewa: Halartar wallafofin majalissar Ahlul-baiti (AS) ta duniya tare da mawallafa daban-daban daga kasashen larabawa, musamman kasashen Masar, Jordan, Morocco, Lebanon, Syria da Palastinu, za su halarci taron zai zama dama mai kyau don kafa sadarwa da hulɗar juna kuma zai iya buɗe sabbin hanyoyin haɗin gwiwa ga masu wallafa da ke cikin taron.

Abun Jan Hankali Anan: wannan taron zaa bude shi a ranar Laraba 11 ga watan Satumba wanda manyan jami'an kasar Iraki da baki na musamman daga kasashe daban-daban za su bude taron baje kolin litattafai karo na 25 a birnin Bagadaza.