Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul-Baiti As - ABNA - ya kawo maku rahoton cewa: a safiyar yau Laraba ne kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta kasar Iraki ta kai wani sabon farmaki a tashar ruwan Haifa da aka mamaye.
Wannan kungiyar ta sanar da cewa a safiyar yau ne ta kai hari tashar jiragen ruwa na Haifa da ke kasar Falasdinu da jirage marasa matuka.
Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta kasar Iraki a cikin sanarwar da ta fitar ta ce ta kai wannan hari ne a matsayin mayar da martani ga laifukan da yahudawan sahyoniyawan suke aikata a kan mata da kananan yara da kuma tsofaffi a Gaza kuma za su ci gaba da kai hare-hare kan wuraren da makiya mamaya suke.
Har yanzu ba a fitar da karin bayani kan farmakin da sojojin Irakin suka kai a safiyar yau a tashar jiragen ruwa na Haifa, wanda kungiyoyin gwagwarmayar yankin suka shafe sama da watanni 11 ana yakin Gaza suna kai farmaki wajen.
A baya dai kungiyar gwagwarmayar Islama ta kasar Iraki ta sanar da cewa za ta zafafa kai hare-hare kan yankunan da aka mamaye domin tallafawa al'ummar Palastinu.
...................................