15 Satumba 2024 - 19:23
Dukkan Mutanen Kauyen “Garyudal” Da Ke Daikundi Sun Yi Shahada A Harin ISIS Suka Kai Afganistan

Ya kalli gidajen kauye sannan ya kalli gawarwakin shahidan. Yana so ya ce in ban da mu maza uku, babu wani mutum da ya tsira a wannan karamin kauye.

Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul-Baiti As - ABNA ya  kawo maku labarin cewa: mutane 14 ne suka yi shahada yayin da wasu 4 suka jikkata sakamakon wani harin ta'addanci da aka kai kan wasu gungun 'yan shi'a a garin "Sangtakht da Bandar" na lardin "Daikundi" tsakiyar Afghanistan.

Wani wanda ya shaida faruwar lamarin ya ce a ranar Alhamis 12 ga watan Satumba shekara ta 2024 da misalin karfe daya na rana mutane 18 daga kauyen "Qariyodal" da ke birnin Sengtakht da Bandar na lardin Daikundi na kasar Afganistan ne suka tarbi matafiya. wadanda suka dawo daga aikin ziyarar Arbaeen, a yayin da suke tafiya a tuddan dake garin Khumsafid "kan iyaka tsakanin Daikundi da Gur". Bayan wucewa ta tsaunin Khumsafid, sai suka shiga yankin lardin Ghor da ke yankin "Palosang", a lokacin ne wasu mutane hudu dauke da makamai a kan babura biyu suka tsayar da wadannan mutane bisa hujjar daukar hoto na rukuni, biyu daga cikinsu sun dauki bidiyo da hotuna, sauran biyun kuma suka bude masu wuta. A sakamakon haka mutane 14 ne su kai shahada wasu 4 sun jikkata.

Ya ci gaba da cewa: Ni da kaina na je wurin da abin ya faru, tare da taimakon wasu muka kai gawarwakin zuwa kauyen. 13 daga cikin shahidan sun fito ne daga Daikundi kuma daga kauyen Qarodal, kuma mutum daya daga lardin Ghor da ya je garuruwan Sangtakht da Bandar da yaje domin ganin likitan hakora.

Shaidar gani da ido ya ci gaba da bada labarin abunda ya gani da idonsa a kauyen Ghariodal kamar haka: Lokacin da na dawo daga "Palo Seng", wani kauye kusa da wurin da abin ya faru, sai dare ya yi. Lokacin da na gangaro daga tudun Khamsafid zuwa ƙauyen Ghoriodal, na ji kamar an tada kiyama ne. Domin daga dukkan gidajen da ke kauyen, ana ji karar kuka da kukan mata da yara. Kusa da ƙauyen naga Husainiyah, na ga gawarwaki 13 a kwance kusa da kusa. Wani abin al'ajabi ne, ban ga kowa ba, a wurin akwai tsofaffi uku ne kawai waɗanda ba su san abin da za su yi ba, wani lokaci sukan shiga cikin Husainiyyar, wani lokaci kuma su fito suna duba gawar shahidan. Na je kusa da daya daga cikin wadannan tsofaffin nan uku na ce: Kawu! bai ji ba Na girgiza masa hannu da kafada, ya kalleni a firgice, amma bai ce komai ba, hawaye na kwararowa daga kwarin idanuwansa. Na ce: Kawu babu mai zuwa ya taimaka maku ne? Bai sake cewa komai ba. Ya kalli gidajen kauye sannan ya kalli gawarwakin shahidan. Kamar Yana so ya ce in ban da mu maza uku, babu wani mutum da ya tsira a wannan karamin kauye. Yayin da karar kururuwa da kukan mata da kananan yara ke fitowa daga gidaje ya rade cikin tsaunukan da ke kewayen Qariodal, lamarin ya haifar da wani yanayi na bakin ciki.

Ya kamata a lura cewa kungiyar ta'addanci ta ISIS ta Khorisan ta dauki alhakin wannan harin ta'addanci ta hanyar fitar da sanarwa.

...................................