Jami'an tsaron gwamnatin Al-Khalifa sun kama wasu
matasa 'yan kasar Bahrain guda hudu wadanda suka halarci tattakin Arbaeen din
Imam Husaini As ba tare da wani dalili na shari'a ba!
Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul-Baiti As - ABNA - ya kawo maku rahoton cewa: Hudu daga cikin wadanda aka kama sune: Ali Baqali daga Sanab, Ibrahim Adil Ibrahim daga Mu’amar, Ali Matrouk da Abbas Muslim daga Karanah.
Babban mai gabatar da kara ya zargi Ebrahim da tayar da tarzoma tare da yanke masa hukuncin daurin kwanaki 15 a gidan yari.