Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul-Baiti
As - ABNA - ya kawo maku rahoto bisa nakaltowa daga shafin sadarwa na IRNA cewa
Jagoran kungiyar Ansarullah ta kasar Yaman ya fara jawabinsa a yau a daidai
lokacin da watan Rabi'ul Awwal ya shiga, inda ya yi bayani kan abubuwan da ke
faruwa a yankin ciki har da Gaza.
Kamfanin dillancin labaran Irna ya habarta cewa, a a yau ranar Alhamis shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen, Sayyid Abdul Malik al-Houthi, a farkon jawabin nasa, ya taya daukacin al'ummar musulmin duniya murnar shigowar watan Rabi'ul Awwal mai alfarma. A kowace shekara al'ummar kasar Yemen na bayar da kulawa ta musamman ga maulidin manzon Allah (S.A.W), kuma a wannan lokaci tana da ayyuka masu fa'ida da dama wadanda suka kunshi na ilimi da jihadi na tsawon makonni.
Sayyid Al-Houthi ya fayyace cewa: "Ya kamata a ba da kulawa ta musamman ga Jihadi da kafirai da munafukai a dukkan bukukuwa da ayyukan maulidin Annabi Muhammad (SAW) a yanayin hare-haren da Amurka da Isra'ila suke kai wa al'ummar Musulmi.
Shugaban na kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen ya jaddada cewa yana da hadari a bar Jihadi a tafarkin Allah a yayin hare-hare da kuma laifuffukan da makiya suka dora kan al'ummar musulmi.
Ya ci gaba da yin tsokaci kan abubuwan da ke faruwa a Gaza inda ya ce: Musulman Gaza na fama da munanan hare-hare da kashe-kashen gilla da Isra'ila ke yi, wanda ke cutar da al'ummomin kasashen da ba musulmi ba.
Ana cikin kammala...