Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul-Baiti
As - ABNA - ya habarto maku cewa: ma’aikatar harkokin cikin gidan kasar ta
Syria ta sanar a cikin wata sanarwa game da harin ta’addanci da aka kai kan
ayarin motocin gwamnan Daraa a kudancin kasar Syria.
A sakamakon wannan harin, 6 daga cikin wanda suke tare da gwamnan sun jikkata. Sai dai ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar ta Syria ba ta ambaci yanayin jikin gwamnan Daraa Loui Khariteh ba.
Kazalika majiyoyin cikin gida sun bayyana cewa ‘yan ta’adda sun yi arangama da jami’an tsaron gwamnan bayan da suka tayar da bam a kan hanyar ayarin motocin gwamnan da abokan tafiyarsa.
A cewar wadannan majiyoyin, shahararren Kanal Al-Muhammad, kwamandan 'yan sandan lardin Dar'a, da Husain Ar-Rifai, shugaban ofishin jam'iyyar Baath na wannan lardin, suna cikin wannan ayarin da ke tare da gwamnan.
Suna kan hanyarsu ta komawa birnin Daraa ne bayan sun ziyarci wasu ayyukan hidima a birnin Harak da ke gabashin lardin Daraa, lokacin da fashewar ta afku suna a kan hanyar Kavaran tsakanin garuruwan Ulama da Kharba Ghazaleh.
Wannan dai shi ne karo na biyu da 'yan ta'adda suka kai wa ayarin motocin gwamnan Daraa hari, a baya 'yan ta'addar sun kai hari kan ayarin motocin Levi Khariteh a kusa da birnin Mohjah da ke arewacin lardin Daraa.
Damascus, babban birnin kasar Syria, yana da nisan kilomita 50 daga arewacin iyakar lardin Daraa, da kuma kilomita 100 daga arewacin birnin Daraa dake kan iyaka da cibiyar lardin.
................