4 Satumba 2024 - 10:33
Hamas Ta Ɗauki Sabbin Sojoji 3,000

Tashar talabijin ta sahyoniya ta 12 ta sanar da cewa bayan fiye da watanni 10 da fara yakin, kungiyar Hamas ta yi nasarar sake gina karfinta a arewacin zirin Gaza.

Kafofin yada labarai na Hebrew: A cewar wannan kafafan yada labarai na Ibraniyawa, kididdigar da ake da ita a yanzu ta nuna cewa Hamas ta yi nasarar daukar tare da tsara sabbin sojoji kusan 3,000 a arewacin zirin Gaza.

Yammacin Gabar Kogin Jodan ya zamo kalubale mai tsanani na sahyoniyawan da ba su da nutsuwa Akanta.

Bisa nakaltowa daga Kamfanin dillancin labaran Quds A safiyar ranar Laraba 4 ga watan Satumba ne gwamnatin yahudawan sahyoniya bayan sun gaji da yakin da aka kwashe watanni 11 ana gwabzawa, inda suka fuskanci kai hari ba kakkautawa daga ƙungiyoyin gwagwarmaya hakan ya tilasta masu gudu zuwa garuruwan Jenin, Tulkarem da Tubas dake arewacin gabar yammacin gabar kogin Jordan, har ma sun kauracewa wasu unguwannin. na wannan yanki kamar Nurshams. Sai dai ba wai wadannan wuraren an kaurace masu ba ne kai harma hare-haren gwagwarmaya ya mamaye a wadannan yankuna, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da dama da kuma jikkata a hannun sahyoniyawa har zuwa wannan lokaci.

Kimanin watanni biyu da suka gabata ne aka gudanar da wani taro a wata kungiyar aiki ta musamman karkashin kulawar majalisar Knesset, kuma sakamakonsa wani muhimmin gargadi ne ga gwamnatin Netanyahu, wanda akai magana da kakkausar murya akan batun yaki. A cikin wannan taron, an gargadi gwamnatinsa game da batu biyu: "Yammacin Kogin Jordan ta yi shiru cikin wutar yaki kuma kungiyar Fatah suna ci gaba da kafuwa".

Yammacin kogin Jordan, wanda a cewar gwagwarmayar Falasdinu, "yanzu ta fara wasanta" a bangaren dabarun yaki, kuma wane fifiko ta ke da shi kan Gaza, inda ya girgiza ginshikan 'yan tsirarun sahyoniyawan a wannan taron?


Wasu fa'idodin dabarun yaki da Yammacin Kogin Jordan ke da shi da suka fi na Gaza:

1- Girman Kasa: Yankin Yammacin Kogin Jordan yana da fadin kasa kimani kilomita murabba'i 5800, ma'ana ya ninka Gaza sau 16 (kilomita murabba'in 360).


2- Cuɗanya da yankunan da aka mamaye: Tsawon shekaru gwamnatin sahyoniyawan a karkashin wata dabara mai suna creeping occupation policy tana kokarin mamaye yankunan Palastinawa kuma a kan haka a duk inda ta samu babu kowa sai ta gina matsuguni kuma wannan siyasar da ba ta dace ba ta kawo al'ummar yahudawan sahyoniya a tsakanin Palasdinawa. A halin yanzu matsugunan yahudawan sahyoniya da ke kewaye da gabar yammacin kogin Jordan su ne mafi girman rauni na yahudawan sahyoniyawan, kuma dukkanin wadannan matsugunan ba su da kariya gaba daya ta fuskar tsaro.

3- Babban fifiko Yawan Jama'a: Dangane da kididdigar hukuma ta baya-bayan nan, yawan mutanen Yammacin Kogin Jordan ya kai kusan miliyan 3 da mutane dubu 250 (a kididdigar ba ta hukuma ba, ya fi yawa), kuma idan aka kwatanta da yawan al'ummar Gaza sama da miliyan 2, ana la'akari da ita a matsayin kasa mai girma da gagarumin fifiko.

4- Tsarin doka mafi karfi: Kasancewar gwamnatin mai cin gashin kanta a yammacin kogin Jordan na tsawon shekaru, tare da duk wata rashin nasara, amma suna da wasu fa'idoji masu anfani, kuma hakan ya kasance cewa tsawon shekaru kungiyoyin masu cin gashin kansu sun nisanta kansu daga jikin al'ummar Falasdinu, sannu a hankali wadannan kungiyoyi sun rasa hadin kan su. A tsawon lokaci, dakarun Fatah (reshen soja na kafa) da suka samu horo da tsari sun shiga cikin masu gwagwarmaya har ta kai da dama suna ganin cewa kungiyar ta Fatah ta kebanta da kafa kanta, wasu kuma na ganin cewa kungiyoyin gwagwarmayar da suke bayyana wanzuwarsu a yau da kullum a Yammacin Kogin Jordan Suna tsammanin sun fito ne daga jikin wannan yunkuri. A halin yanzu dai akwai dakaru a cikin kungiyar Fatah masu kishin gwagwarmaya da manufarsu da kuma taimakawa gwagwarmayar Palasdinawa.

Saboda yanayin da aka ambata, gudanar da ayyukan gwagwarmaya na daidaikun mutane a Yammacin Kogin Jordan da yankunan da aka mamaye yana da sauki sosai kuma yana dauke da adadin nasara mafi girma, kuma wadanda aka kashe da fursunonin yahudawan sahyoniya sun fi yawa a yakin da ake yi da yammacin kogin Jordan.

Ba kamar Gaza ba, mafi girman yanki a yammacin gabar kogin Jordan tare da hanyoyi masu yawa, ƙauyuka da garuruwa masu nisa da juna ya sa ya zama mafi wahala ga Sahayoniyawa wajen sarrafawa, murkushewa da gudanar da ayyuka, kuma idan yammacin kogin Jordan, wanda shine a halin yanzu da makami za su shiga fagen fama da yawa, aikin sahyoniyawan a tsakiyar yankunan da aka mamaye zai kasance mai matukar wahala da sarkakiya.

Wadannan watanni 11 da aka kwashe ana yaki sun cinye duk wani karfi da kayan aiki da kayan aikin soja na wannan gwamnati, kuma ana iya ganin wannan a fili daga rashin karfin soja, jajircewar aikin soja, karuwar hasarar rayuka, rikicin da ya barke tsakanin al'ummar kasar na majalisar yaki, manyan jami'an gwamnati sun shiga rudani a cikin al'ummar Sahayoniya.

A daidai lokacin da rayuwar gwamnatin sahyoniyawan ke kan tabarbarewa tare kuma da sake bunkasar gwagwarmaya a yammacin gabar kogin Jordan tare da wadannan yanayi na iya haifar da mummunan rauni na karshe a jikin yahudawan sahyoniyawan.

A halin da ake ciki a halin yanzu mafi karancin yunkuri a yammacin gabar kogin Jordan, wanda a halin yanzu ake gwabzawa da kashi 10% na karfinsa, zai haifar da sakamakon barakar da kungiyar Hizbullah ta samarwa yahudawan sahyuniya a arewacin yankunan da aka mamaye. A matakin farko zai haifar da kauracewar matsugunan da ke kewayen gabar yammacin Jodan za su rage yawan jama'a, kuma idan aka ci gaba, za a wargaza kewanyar da akaiwa Gaza, kuma Sahayoniyawan, idan suna da hankali, za su nemi amincewa da sulhu.