Kafofin yada labaran Afghanistan
sun ce harin ya faru ne da tsakar ranar Alhamis a yankin Karyudal da ke kan
iyaka tsakanin lardin Daykundi da Ghor.
Rahotanni sun nuna cewa wadanda harin ya rutsa da su 'yan Shi'a ne daga gundumar Sang Takht da ke lardin Daykundi, wadanda suka je garin Karyudal domin ganawa da 'yan uwansu da suka dawo daga ziyarar Arbaeen a birnin Karbala na kasar Iraki mai tsarki.
Rahotanni sun ce maharan sun dakatar da wata motar safa da ke dauke da mutanen da sunan daukar hotuna sannan suka bude musu wuta.
Wata majiya a lardin Daykundi da ta bukaci a sakaya sunanta saboda dalilai na tsaro, ta shaidawa kamfanin dilancin labaren AFP cewa mutane 14 ne suka mutu yayin da wasu akalla hudu suka jikkata a harin.
Har yanzu gwamnatin Afghanistan ba ta fitar da wata sanarwa game da harin ba.
A Afghanistan, kungiyoyi daban-daban masu dauke da makamai da suka hada da Daesh/ISIS sukan kai wa 'yan Shi'ar Afganistan hari da munanan hare-haren bama-bamai.