Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul-Baiti As - ABNA ya kawo maku labarin cewa: bayan harin
ta'addancin da aka kai kan mabiya mazhabar Shi'a a garin Daikundi na kasar
Afganistan, wanda ya yi sanadin shahadar mutane 14, an samu martani da dama
daga daidaikun mutanen kasar Afghanistan da na sauran kasashen duniya da sauran
kungiyoyi, wanda zaku iya karantawa a kamar haka a ƙasa:
Ma'aikatar harkokin wajen Iran a yayin da take goyon bayan matakan yaki da ta'addanci na jami'an kasar Afghanistan, ta bukaci daukar matakan gaggawa na hukunta wadanda suka aikata wannan laifi.
Majalisar malaman Shi'a ta kasar Afganistan ta bukaci jami'an tsaron kasar da su gaggauta kamo wadanda suka aikata wannan danyen aiki tare da hukunta su kan abin kunya da suka aikata.
Ofishin jakadancin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da ke birnin Kabul ya bukaci a hukunta wadanda suka aikata wannan babban abin takaici tare da bayyana shirinsa kan hakan.
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya ya kira ruwan harbe-harben da akai akan ‘yan Shi’a a Daykundi a matsayin “mummunan aiki” inda ya bukaci a gudanar da cikakken bincike tare da hukunta wadanda suka aikata wannan laifi.
Kungiyar kare hakkin bil'adama ta ce a martanin da ta yi game da harbe-harben 'yan Shi'ar Daikendi: Al'ummar Hazara na Afghanistan na bukatar karin kariya.
Ofishin jakadancin Japan da ke Kabul ya kira wannan harin ta'addanci tare da neman a dakatar da irin wannan lamari cikin gaggawa.
Richard Bennett, wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman kan kare hakkin bil'adama a Afghanistan, ya yi Allah wadai da kisan kiyashin da aka yi wa 'yan Shi'a a Daikundi da cewa yana nuni da faruwar "laifi na kasa da kasa".
A yayin da ake yin Allah wadai da wannan harin ta'addanci, ofishin UNAMA da ke birnin Kabul ya bukaci da a gudanar da cikakken bincike kan wannan harin tare da ganowa da hukunta wadanda suka kai harin.
Abdullah Abdullah, tsohon shugaban kwamitin sulhu na kasa a Afganistan, ya bayyana harin na Daikundi a matsayin zalunci, ya kuma jajantawa iyalan wadanda harin ya rutsa da su.
Muhammad Muhaghegh shugaban jam'iyyar hadin kan Islama ta kasar Afganistan ya dauki wannan lamari a matsayin ci gaba da kashe-kashen Hazara da 'yan Shi'a a Afganistan tare da dora alhakin hakan kan 'yan Taliban din.
Zabihullah Mujahid, kakakin gwamnatin Taliban ya kira wannan harin a matsayin "abin dabbacin" tare da bada tabbacin cewa za a kama wadanda suka kai harin tare da hukunta su.
...................................
#harin ta'addancin akan #'yan Shi'ar #Daikundi kasar #Afganistan