23 Oktoba 2019 - 11:21
​Musawi: Wasu Kasashe Na Kokarin Ganin An Samu Fahimtar Juna Tsakanin Iran Da Saudiyya

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Sayyid Abbas Musawi ya bayyana cewa, wasu daga cikin kasashe na kokarin ganin sun shiga tsakani domin ganin an samu fahimtar juna tsakanin Iran da Saudiyya.

(ABNA24.com) A lokacin da yake zantawa da wata kafar yada labarai a birnin Tehran, Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Sayyid Abbas Musawi ya bayyana cewa, wasu daga cikin kasashe sun tuntubi Iran, wasu ma jami’ansu sun zo har Iran domin tattaunawa da jami’an kasar, kan yadda za a samu hanyoyin warware rashin fahimtar juna tsakanin manyan kasashen gabas ta tsakiya guda biyu, wato Iran da kuma Saudiyya.

Musawi ya ce, Iran tana maraba da wannan kokari, kuma warware duk wani sabani da rashin fahimta tsakanin Iran da Saudiyay ya zama wajibi, kasantuwar wadannan kasashe biyu su ne manyan kasashen yankin, kuma su ne manyan kasashen musulmi masu babban tasiri.

Ya ce Iran ta riga ta bayyana matsayinta kan wannan batu, kuma tana fatan Saudiyya da dukkanin sauran kasashen yankin za su amince da shawarar da Iran ta gabatar, ta hada kai tsakanin dukkanin kasashen yankin, domin yin aiki tare da juna a dukkanin bangarori, domin hakan shi ne zai amfane su kuma ya amfani al’ummominsu.

........
340