14 Oktoba 2019 - 04:40
Shugaban Kasar Rasha Viladmir Putin Zai Kai Ziyara Kasar Saudiya A Gobe Litinin

Rahotanni sun bayyayan cewa shugaban kasar Rasha putin zai kai ziyara kasar Saudiya babbarkawar Amurka a gobe litinin in Allah ya kaimu, da zimmar neman bashi damar shiga tsakani domin kawo sulhu tsakanin Tehran da birnin Riyad,da danganta tayi tsami tsakaninsu.

(ABNA24.com) Rahotanni sun bayyayan cewa shugaban kasar Rasha putin zai kai ziyara kasar Saudiya babbarkawar Amurka a gobe litinin in Allah ya kaimu, da zimmar neman bashi damar shiga tsakani domin kawo sulhu tsakanin Tehran da birnin Riyad,da danganta tayi tsami tsakaninsu.

Hakan yana a matsayin wani kokari ne na amafani da hanyar diplomasiya da kasar Rasha takeyi wajen daidaita dangantakarta da sauran kasahen yankin gabas ta tsakiya.

Wannan ziyara ta Putin ta zo ne jim kadan bayan da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya sanar da aikewa da sojoji3000 da wasu karin jiragen yaki masu saurkar Uguluzuw kasar Saudiya, domin dakile abin da ya kira barazanar Iran, biyo bayan hari da jirgin sama marasa matuki da mayakan kungiyar huthi ta kasar yamen suka kai a matatar samar da man fetur ta Saudiya a kwanakinbaya. Hakan ya jawo tsaiko sosai a bangaren samar da makamashi a duniya.,

Amurka ta yi amfani da wasu kawayenta na turai wajen zargin Iran da hannu wajen kai harin. Zargin da mahukumtan Tehran suka musanta tare da bayyana shi amatsayin mara tushe balle makama.



/129