(ABNA24.com) Wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton na kungiyar ISWAP ne dake kiran kanta reshen kungiyar IS a yammacin Afrika sun kashe sojoji uku da kuma fararen hula hudu a wasu jerin hare hare a arewa maso gabashin Najeriya.
Majiyoyi daga yankin sun shaida wa kamfanin dilancin labaren AFP, cewa, mayakan sun kai hari ne a wani shingen binciken soji dake birnin Gajiganna a kilomita kimanin hamsin daga Maiduguri babban birnin jihar Borno da yammacin jiya Juma’a.
Hare haren na zuwa ne kwana guda, bayan wani mummunan fada da aka gwabza tsakani dakarun hadin guiwa na yankin dake yaki da mayakan dake ikirari da sunan jihadi da kungiyar ISWAP, a kewayen garin Monguno dake jihar Borno, inda sojojin Chadi biyu da kuma mayaka da dama suka mutu.
Rikicin boko haram da aka kwashe shekara goma ana yi ya dai yi sanadin mutuwar mutane 35,000 tare da cilastawa wasu kimanin miliyan biyu tserewa daga muhallensu, mafi yawa a yankin arewa maso gabashin Najeriya, rikicin da daga bisani ya baru, zuwa kasashe makobta kasar da suka hada da Nijar, Chadi da kuma Kamaru.
/129
13 Oktoba 2019 - 04:46
Lambar labari: 982142
Wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton na kungiyar ISWAP ne dake kiran kanta reshen kungiyar IS a yammacin Afrika sun kashe sojoji uku da kuma fararen hula hudu a wasu jerin hare hare a arewa maso gabashin Najeriya.