5 Agusta 2019 - 07:11
Najeriya: 'Yan Bindiga Sun Kashe Shugaban Miyatti Allah Na Jihar Adamawa

Rahotanni da ke fitowa daga Nigeria sun bayyana cewa wasu yan bindiga da ba’a san ko su waye ba sun kai masa hari a gidansa dake Mayo- Belwa dake kudancin jihar Adamawa, ...

(ABNA24.com) Rahotanni da ke fitowa daga Nigeria sun bayyana cewa wasu yan bindiga da ba’a san ko su waye ba sun kai masa hari a gidansa dake Mayo- Belwa dake kudancin jihar Adamawa, jami’in hulda da jama’a na kungiyar Miyati Allah reshen jahar Adamwa Mohammad Jika Buba ya bayyana cewa suna kyautata zaton wadanda suke garkuwa da mutane ne domin karbar fansa, a yankunan dake kudanci Adamwa ne suka kasha shi,

Shi dai Saidu Kolako yana daga cikin shuwagabanin Alumma a cikin jihar da hukumar yansandata basu lambar yabo ta jinjina game da namijin kokarin da suke yi wajen taimakawa yan Sanda wajen yaki da bata gari dake tafka muggan laifuka.

To sai dai wannan ya na zuwa ne adai dai lokacin da tsohon shugaban Nigeria Olushegun Obasanjo yayi wata ganawa da shuwagabannin Fulani dake kudu masu yamma na Nigeria da suka kunshi jihohin Kwara Kogi a kokarin da yake yin a ganin an kawo karshen rashin tsaro da yankin ke famadashi dama Nigeria baki daya.



/129