Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Bayt (AS) – ABNA – ya ruwaito cewa: Ayatullah Sayyid Mojtaba Khamenei, Jagora Mai Girma na Juyin Juya Hali, a amsa ga wasiƙun gungun ɗalibai daga duk faɗin ƙasar Iran da suka aika masa cikin watannin da suka gabata, ya ɗauki ƙuduri da nufi da jin nauyin da suke da shi na gina makoma a matsayin igiyar haɗin "alƙawari" tsakanin jagoranci da matasa kuma ya nanata wajibcin yin tattali da tanadin makamin ilimi da imani da tsarkake zuciya da ƙara ƙoƙari wajen ƙara ƙarfi da ikon Iran.
Rubutun amsar Jagora Mai Girma yazo kamar haka:
Bismillahir Rahmanir Rahim
Sallama ga 'Ya'yana Ababen Ƙaunata;
Na karanta wasiƙunku masu cike da ƙauna. Ina godiya ga yalwar alherinku ɗalibai matasa masu ƙwazo kuma zan yi muku addu'a ta musamman ga dukanku waɗanda kuka ɗora wani nauyi a wuyana.
A cikin wasiƙunku da na yawancin matasa da ɗalibai waɗanda ke sani cikin alheri da ƙaunarsu, akwai hasken ƙuduri da nufi da jin nauyin gina makoma.
Wannan ƙaƙƙarfan alkawari, amana ce mai nauyi wadda ta samo asali daga makarantar Musulunci tsantsa ta Muhammadu (S.A.W) da gadon Khomeini Mai Girma da Khamenei Shahidi (Allah ya ɗaukaka matsayinsu) kuma ita ce igiyar haɗin "alƙawarinmu" da juna.
Don wannan manufa, duk abin da za ku iya ku yi wa kanku tattali da makamin ilimi da imani da tsarkake zuciya da zumunta da Allah da zurfin sanin ilimomin Alkur'ani da Ahlul-Bayt (A.S) kuma da aiki da ƙirƙira ninki biyu ku ƙara ƙarfi da ikon Iran abar ƙauna domin da addu'ar shugabanmu mai kaunarmu (Allah ya gaggauta bayyanarsa) da tafiya kan tafarkin sojoji masu alƙawari zuwa kololuwar ci gaba da wayewar musulunci da Iran ta fi kyau da sauri ta tabbata, in Allah ya so.
Sayyid Mojtaba Hosseini Khamenei
6/Aban/1405
Ra'ayinka