25 Yuli 2019 - 06:56
​Iran: Shugaban Majalisar Tsaron Kasa Ya Gana Da Tawagar Hamas

Shugaban majalisar tsaron kasa a Iran Ali Shamkhani ya gana da tawagar kungiyar Hamas a Tehran.

(ABNA24.com) Tashar Almayadeen ta bayar da rahoton cewa, a yau shugaban majalisar tsaron kasa a Iran Admiral Ali Shamkhani ya gana da tawagar Hamas karkashin jagorancin Saleh Al-aruri mataimakin shugaban kungiyar ta Hamas a birnin Tehran.

A yayin ganawar Shamkhani ya bayyana cewa, dukkanin kutunguilar da wasu daga cikin sarakunan larabawa ‘yan kanzagin Amurka a gabas ta tsakiya suka yi ta kullawa domin rusa alaka tsakanin Iran da Falastinawa, hakan ya ci tura.

Ya ce batun goyon bayan Falastinawa da kuma taimaka musu a wurin Iran lamari da addini da ‘yan adamtaka, saboda haka babu batun ja da baya a cikinsa.

A nasa bangaren shugaban tawagar kungiyar Hamas da ke gudanar da ziyara a kasar Iran Saleh Alaruri ya bayyana cewa, dukkanin ci gaban da Falastinawa suka samu ta fuskoki daban-daban musamman a bangaren samun sabbin hanyoyi da kayan aiki wajen kare kansu, hakan kokari ne na kasar Iran, wanda Falastinawa ba su taba mantawa da hakan ba.



/129