23 Yuli 2019 - 04:28
​Nijar Ta Kwaso ‘Yan Kasarta 900 Daga Libiya

Hukumomi a Jamhuriyar Nijar sun kaddamar da wani shiri na mayar da 'yan kasar bakin haure da masu ci rani gida, bayan sun shafe lokaci suna tsare a cibiyoyin da aka tsugunar da bakin haure a kasar Libiya.

(ABNA24.com) Hukumomi a Jamhuriyar Nijar sun kaddamar da wani shiri na mayar da 'yan kasar bakin haure da masu ci rani gida, bayan sun shafe lokaci suna tsare a cibiyoyin da aka tsugunar da bakin haure a kasar Libiya.

Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa na AFP ya bayar da rahoton cewa, wadanda aka dawo da su daga Libiya 'yan asalin jihohinTahoua daZinderne wadanda dukkaninsu suka jima a hannun jami'ai da ke kula da cibiyoyin tare jama'a bakin haure da 'yan ci rani a kasar Libiya.

Akalla 'yan ci rani 900 ne 'yan asalin Jamhuriyar Nijar da ake rike da su a cibiyoyin tsarebakin haure a kasar Libiya suka koma gida, daga farkon watan Janairun wannan shekarar zuwa yanzu kamar yadda wata majiya daga hukumar kula da kaurar jama'a ta MDD OIM ta bayyana.

Ko a ranar Juma'ar da ta gabata ma wani jirgi shake da yan ci rani daga kasar ta Libiya ya sauka a birnin Yamai dauke da bakin haure 147 ciki har da wasu kananan yara tara.



/129