15 Afirilu 2019 - 17:13
Sojojin Chadi sun kashe 'yan Boko Haram 63

Akalla mayakan Boko Haram 63 sun rasa rayukansu a wani dauki-ba-dadi da sojojin Chadi a cikin daren da ya gabata.

Mai magana da yawun sojin kasar, Kanar Azeem Bermandoa ya ce, an kashe musu jami’ai bakwai tare da jikkata 15 a harin da mayakan na Bokio Haram suka kaddamar kan sansanin sojin da ke Bouhama a yankin Tafkin Chadi.

Bermandoa ya kara da cewa, a halin yanzu suna kan farautar sauran mayakan na Boko Haram bayan sun kashe 63 daga cikinsu.

Ko a  watan jiya, sai da Boko Haram ta kashe sojoji 23 a Yankin Tafkin Chadi, harin da ake kallon sa a matsayin mafi muni da kungiyar ta kai kan dakarun sojin Chadi.