Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Bayt (AS) – ABNA – ya ruwaito cewa: Maulidin bana ya zo da sabon salo, inda aka rarraba sabbin mashinan hawa ga masu ɗauke da sunayen Manzan Allah (S), Imam Ali (AS), Imam Hassan (AS), Imam Husaini (AS), da kuma Sayyidi Abdullahi da Sayyid Abudalib.
Haka kuma, an rarraba kayan ɗaki ga masu sunayen Sayyida Amina, Sayyida Fatima da Sayyida Khadija (AS). Bugu da ƙari, an rarraba buhunan shinkafa sama da 200 ga mabukata domin tallafa musu.
A yayin taron, an kuma karrama masu sunayen Khalifofin Manzan Allah, daga Imam Ali har zuwa Imam Mahdi (AS), inda aka ba kowannensu kayayyaki na musamman, ciki har da kyautar kuɗi Naira 300'000.
A wajen wannan Maulidi, an kuma gwangwaje S. Uziri da babban gida na musamman.
An gabatar da abubuwa da dama a wajen wannan gagarumin Maulidi, waɗanda insha Allah za mu ci gaba da kawo muku a hankali a wannan shafin na SK PRESS TV.
Wakilan SK PRESS TV sun samu halartar wannan gagarumin taro, kuma wannan shi ne rahotonmu na farko daga wajen Maulidin.
Ga wasu daga cikin hotunan taron.
Rahoto: Sk Press Tv
Ra'ayinka