Shugaban na kasar Iran ya bayyana haka ne a jiya Lahadi da yake bude sabbin wuraren hakar iskar Gas, dake kudancin kasar sannan kuma ya ce; Wannan rana ce ta farin ciki domin kuwa tana a matsyin nasara akan abokan gaba da basu son ci gaban Iran.
Dr. Hassan Rauhani ya kuma bayyana cewa; Makiya sun tsammaci Iran za ta mika wuya saboda matsin lambar da masu girman kai na duniya suke yi mata, amma al’ummarmu wacce a tsawon tarihi ta yi tsayin daka, tana ci gaba da samun nasarori.