21 Agusta 2026 - 00:09
Source: ABNA24
Sheikh Yakub: Manzon Allah Ne Ya Kafa Tushen Yaɗuwar Addinin Musulunci

“Ko ba komi kamin Manzon Allah (S) ya zo Madina, tuni ta karɓi musulunci, musulunci ya yaɗu a cikin Madina, saboda haka ko sadda ya zo, ba ya zo ba ne a matsayin ɗan gudun hijira ba, ya zo ne da sunan Shugaba, saboda baki ɗaya Madina maza da mata duk sun karɓi musulunci.

Daga nan Manzon Allah (S) ya zama shi ne Jagora, daga nan kuma ya kafa tushe na yaɗuwar wannan addinin, kuma sai ya zama Allah (T) ya ɗora mashi aiki, irin wanda bai taɓa ɗora wa wani Manzo ba.

(وَمَا أَرْسَلْنَاكَ إِلَّا كَافَّةً لِّلنَّاسِ بَشِيرًا وَنَذِيرًا). 

Ma'ana “Bamu aiko ka ba sai ga dukkanin mutanen duka duniya”, walau mutum yana Asia ne, ko yammacin Turai, ko yana arewacin Afrika, ko yana tsakiyar Afirka ta Kudu ne, ko ina yake, Fari ne, Baki ne, idan akwai Tsanwa ko shi Tsanwan ne, ko shi wane iri ne, to an aiko manzon Allah (S) gare shi.

Ba bu wani Manzon da aka yi wa irin haka, sannan kuma da Aljannu, da bamu ganin su, su suna ganin mu, to su ma an kallafa masu suyi imani da shi, har ma akwai “Suratul Jinni” su waɗannan aljanun farare ne, baƙaƙe ne, jajaye ne, Ifiritu-Minal-Jinni ne, duk wajibin su suyi imani da shi. Ba bu wani annabin da aka ɗora ma wannan aikin sai shi kaɗai.

__Wani ɓanagre na jawabin, Sheikh Yakub Yahya Katsina, a wajen Mauludin Manzon Allah (S) na Halkar Rasulil-Akram (Zone A). 

20/08/2026..

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha