Rahoton da aka wallafa a jiya Lahadi, ya nuna cewa an samu karin kashi 11 cikin 100 na fararen hular da suka hallaka a kasar ta Afghanistan da yawansu ya kai dubu da 804, wasu dubu 7 da 189 kuma suka jikkata, idan aka kwatanta da adadin shekarar 2017.
A shekarar ta 2018 kadai, hare-haren kunar bakin wake sau 65 aka kai a sassan Afghanistan, mafi akasarinsu a babban birnin kasar Kabul, inda hare-haren suka yi sanadin mutuwar sama da fararen hula dubu 2 da 200.
A gefe guda kuma rahoton ya ce, hare-haren hadin gwiwa na jiragen yakin Amurka da sojin kasar sun hallaka mutane 500 a shekarar ta 2018.
Rahoton, ya zo ne dai dai lokacin da ake sa ran a yau wakilan Amurka, da na kungiyar Taliban za su gana a Doha babban birnin kasar Qatar don kawo karshen yakin da suke gwabzawa.
A cewar Majalisar dinkin duniya, a cikin shekaru 10 da suka gabata kadai, fararen hula dubu 32,000 suka hallaka a yakin Afghanistan, wasu akalla dubu 60 kuma suka jikkata.
A halin da ake ciki shugaban Amurka Donald Trump ya dukufa wajen kawo karshen yakin da Amurka ta ke yi da al-Qa’eda, Taliban da kuma ISIS a kasar ta Afghanistan, inda yake fatan janye dakarun Amurkan dubu 14 da ke kasar.