Da yake sanar da hakan kwamishinan kwamitin sulhu na Tarayyar Afrika Smail Chergui, ya yi kira ga kasashen, wandanda bai bayyana sunayensu ba, da su daina tsoma baki cikin harkokin kasar ta Libiya.
Yayin wani taron manema labarai da ya gudana a gefen taron na (AU) na 32, da ya gudana a birnin Adis-Ababa na kasar Habasha, Mista Chergui, ya ce al'ummar Libiya sun sha wahala sosai sakamakon yakin basasa da tsoma baki da kasashen duniya masu karfi suka yi cikin harkokin cikin gidan kasar, yana mai bukatar a dakatar da duk wani tsoma baki da ba a bukata nan take.
Daga dai daga cikin batutuwan da sabon shugaban kungiyar ta (AU) na wannan karo, kaan shugaban kasar Masar, Abdel Fatah Al-Sisi, ya sanya a gaba akwai matsalar tsaro da yaki da ta'addanci da kuma halin da kasar ta Libiya ke ciki.
Kasar Libiya dai ta fada cikin rikici ne tun bayan kifar da gwamnatin Mirigayi Mu'ammar Ghaddafi a cikin shekara 2011, inda yanzu haka kasar ke fama da gwamnatoci guda biyu.