Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayar da rahoton cewa, dakarun na kasar Masar sun kddamar da wannan harin ne da jijjifin safiyar yau, biyo bayan harin da aka kai jiya akan wata motar bas da take dauke da wasu 'yan yawon bude 'yan kasashen ketare, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar wasu daga cikinsu.
Ma'ikatar harkokin cikin kasar Masar ta ce a jiya Juma'a 'yan ta'addan sun kai hari kan motar bas din wadda take dauke da 'yan kasar Viatnam su 14, inda 3 daga cikinsu gami da wani dan kasar Masar mai yi musu tafinta suka rasa rayuansu, sauran kuma suka samu munanan raunuka.
Har yanzu babu wata kungiya ko wani mutum da ya dauki alhakin kai harin bam din, amma dai tuni mahukuntan kasar ta Masar suka dora alhakin hakana kan 'yan ta'adda masu dauke da akidar wahabiyah takfiriyya da suke da alaka da alkaida, wadanda suke kai hare-hare kan jama'a da sunan jihadi.
Kasar Masar dai na daga cikin kasashen da suke fuskantar ayyukan ta'addanci a lokutan baya-bayan nan, tun bayan da kasar ta zama wata bababr tungar da ake tattara 'yan ta'adda daga kasashe daban-daban domin tura zuwa kasar Syria da Iraki domin kai hare-hare da sunan jihadi, inda gwamnatin Muhammad Morsi ta bayar da dama ga dubban 'yan ta'adda domin su bi ta hanyar kasar Masar domin zuwa Iraki da Syria, musamman daga kasashen Libya da Tunisia.