Tattaunawar wadda Majalisar Dinkin Duniya ke shiga tsakani, na samun halartar bangarorin dake rikici a kasar ta Yamen, da suka hada da 'yan Houtsis da kuma gwamnati mai murabus.
Rikici na tsakanin bangarorin biyu dai ya jefa wannan kasar ta Yemen a cikin bala'i mafi muni a duniya inda mutane kimanin miliyan 14 ke fusknatar barazanar yunwa a cewar MDD,
Wanann dai ba shi ne karo na farko da bangarorin ke haduwa kan teburin tattaunawa ba, don ko a shekara 2016 sun yi wata tattaunawa ta tsawan kwanaki 108 a kasar Koweit , saidai aka watse ba tare da cimma wata matsaya ba.