26 Nuwamba 2018 - 10:58
Sojoji Hudu Sun Mutu A Sakamakon Wani Hadarin Helikofta

Gwamnatin Turkiyya ta sanar da mutuwar sojinta hudu a wani hatsarin jirgin soji mai saukar ungulu a tsakiyar birnin Santambul.

Sanarwar da gwamnatin Santambul ta ce jirgin ya bigi wani gini ne mai hawa hudu a wata unguwa, lamarin da ya yi sanadin mutuwar soji hudu da kuma raunata wani guda.

Ministan tsaron kasar wanda ya ziyarci inda lamarin ya auku, ya ce an bude bincike domin samun karin bayyani akan musababin faduwar jirgin.