Cikin sanarwar da kakakin rundunar sojin Najeriyar Birgediya Janar Texas Chukwu ya fitar, daga ranar 1 ga watan Agusta na 2018 da muke ciki, Manjo Janar Abba Dikko, zai maye gurbin Manjo Janar Rodgers Nicholas a matsayin sabon kwamandan rundunar Operation lafiya dole.
Sai kuma Manjo Janar C.O Ude da zai maye gurbin Manjo Janar Lucky Irabor, a matsayin sabon kwamandan rundunar hadin gwiwar kasashen da fama da rikicin Boko Haram da ke Hedikwata a Ndjamena, babban birnin kasar Chadi.
Sauye-sauyen sun zo ne, makwanni biyu ko kasa da haka, bayan hare-haren da mayakan Boko Haram suka kai kan sansanonin sojin Najeriya da ke Bama a jihar Borno da kuma Jilli a Yobe.
Zalika a lahadin da ta gabata, wasu dakarun Najeriyar da ke karamar hukumar Tarmuwa sun tsira daga wani kwanton bauna da mayakan na Boko sukai musu.
A baya bayan nan dai rundunar sojin Najeriya ta samu nasarori da dama kan mayakan Boko Haram, wanda hakan ya rage karfin kungiyar ta yadda a mafi akasarin lokuta ta ke amfani da 'yan kunar bakin wake, wajen kai hare-hare, a maimakon samamen da takan kai a baya, inda ta ke yin nasarar kwace wasu yankuna a shekarun baya.
28 Yuli 2018 - 16:20
Lambar labari: 903406
Rundunar sojin Najeriya, ta sanar da yin garambawul ga shugabancin sassanta, musamman rundunar ta da ke yakar kungiyar Boko haram ta 'Operation Lafiya Dole'.