Babu Wata Rashin Jituwa Tsakanina Da Daya Daga Cikin Masu Canja Shekar,
Ina fatan alkhairi ga 'yan majalisar APC wadanda suka canja sheka zuwa PDP a yau kuma jam'iyyar APC ta yi iyakacin kokarinta wajen ganin ba su fice daga jam'iyyar ba, don haka ina jinjinawa shugabannin APC bisa kokarin da suka yi na hada kan 'ya'yan jam'iyyar.
Ina da tabbacin cewa wannan mataki da 'yan majalisar suka dauka ba zai cutar da farin jinin jam'iyyar ba saboda haka ina kira ga sauran 'ya'yan jam'iyyar kan kada su tayar da hankulansu, don dama a kan samu irin wannan yanayin da zarar lokacin zabe ya karato.
Na san cewa mafi yawan 'yan majalisar masu canja shekar, suna da matsaloli a mazabunsu musamman ma a bisa tsarin karba karba da na dakatar da shi za suga kamar za'a bararmusu da garinsu ne.
Ina jaddada cewa babu wata rashin jituwa kai tsaye tsakanina da daya daga cikin masu canja shekar kuma ni ban riki daya daga cikinsu a cikin zuciyata ba.
25 Yuli 2018 - 18:38
Lambar labari: 903070
MARTANIN SHUGABA BUHARI GA 'YAN MAJALISAR APC DA SUKA KOMA PDP: