Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Bayt (a.s) – ABNA – ya bayar da rahoton cewa: Wannan maganar da ake yi cewa “Kada a yi Mauludi domin bidi’a ne”, to wannan bidi’ar ta fara mutuwa bidi’ar ‘yan bidi’a. Har ma waɗanda suka kawo bidi’ar cewa “kar a yi Mauludi”, su kansu suna da bidi’a nasu. Amma yanzu ta fara mutuwa, ta nuna ba bidi’a akeyi ba, ashe? Da bidi’a ake yi, da yanzu tuni ta mutu.
Su sun yi amfani da lasifika, sun yi amfani da rediyo, sun buga a jarida, sun yi wa’azin ƙasa ga baki ɗaya, sun yi na yanki, sun yi na jiha, amma duk da haka Mauludin ya ci gaba… To ku gani yanzu, ta nuna su ne ‘yan bidi’a.
Duk abin da bai dace ba, kuma duk abin da babu Allah cikinsa, ba ya son a liƙa shi ga Manzon sa. Ko an fara shi, sai ya ƙare, sai ya zo ƙarshe. A cikin jawabin nasa, har ya ba da misali da wani ɗan bidi’a, inda abokansa suka ce masa: “Ya akayi ba a yi maka ɗinkin Mauludi ba?” Sai ya ce musu: “Babana ne bai son Annabi (SAWW)”. Ashe akan kunnen ubansa aka yi haka. Sai aka ce masa: “A’a, yaka, kai kana son Annabi, aje a yi maka ɗinkin Mauludi da komai da komai”.
Ai wasa guri gare shi ka taɓa darajar Manzon Allah, ka zauna lafiya? To, ku dai gani yanzu, mun wayi gari bidi’o’in nan sun fara ƙarewa. Idan wannan abin (Maulud) da muke yi bidi’a ne, to tuni ya samu karɓuwa.
Rahoto: Hassan Midiya Katsina
……………
Ra'ayinka