Mutanen da aka kama sun hada malaman makarantu 9, sai sojoji 25 da manyan jami'an yansandan sojoji 7.
Mahkuntan kasar ta Turkiya sun sanar da cewa jumillar wadanda aka kame saboda alakarsu da kungiyar Gulan sun haura 170,000. Bugu da kari an zargi mutanen da hannu kai tsaye ko kuma ta bayan fage a juyin mulkin da bai yi nasara ba a shekarar da ta gabata.
A yayin yunkurin juyin mulkin wanda bai yi nasara ba a watan Yuli, an kashe mutane 249 da kuma jikkata wasu budu biyu.
18 Maris 2018 - 14:36
Lambar labari: 886155
Babban mai gabatar da kara da kasar Turkiya ne ya ba da umarnin kama mutane 206 bisa zarginsu da ake yi da alaka da kungiyar nan ta malamin addinin kasar da ke zaune a Amurka, Gulan