Sheikh Ibrahim Zakzaky ya gana da manema labaru ne shekaru biyu bayan da aka tsare shi. Jagoran harkar musuluncin a Najeriya ya ce; Yana samun sauki kuma likitansa ne ya duba shi,
Gabanin wannan lokacin likitocin da jami'an tsaron suke kawo ne ke duba shi, kamar yadda Sheikh din ya ambata, sai dai a wannan karon ya ki amincewa da hakan.
A cikin kwanakin bayan nan an rika yada jita-jita akan yanayin lafiya na sheikh din, wanda ta kai ga yada karyar cewa ya rasu.
Tun a shekarar da ta gabata ne dai kotu a birnin tarayya ta yanke hukuncin a saki shehin malamin kuma a biya shi diyya.