Bayan saukarsa a filin jirgin Djori Hamani na birnin Yamai a jiya Juma'a, shugaban Faransa Emmanuel Macron ya samu tarba ta musaman daga takwaransa na Nijar Issoufu Muhammadu, inda kuma kai tsaye ya nufi sansanin sojin Faransa da ke cikin filin jirgin saman.
Kafin wucewar shugaban na Faransa zuwa sansanin sojin sai da su ka yi wata ganawa mai tsayi tare da shugaba Issoufu na Nijar.
Bayan ziyarar Macron a Gao , Ouagadougou da kuma Abidjan, ziyarar Macron a Jamhuriyyar Nijar ya nuna yadda shugaban ke da fatan ganin kasashen yammacin Afrika sun samu ci gaba tare da yakar ayyukan ta’addanci.
Ziyarar ta Macron za ta kai har zuwa ranar Kirsimeti inda zai gudanar da bukukuwan Kirsimetin tare da dakarun sojin Faransar da ke yaki da ta’addanci a Kasar.