Ayatullah Muhammad Ali Muwahhidi Karmani ya yi kira ga musulmi sunna da shi'a da suka kama hannuwan juna su fuskanci makiyan al'uumar musulmi, tare da yin tsayin daka da kuma gwagwarmaya.
Ayatullah Muhammad Ali Muwahhidi Karmani ya kara da cewa; Bai kamata shi'a da sunna su bari makiyan musulunci su yaudare su ba, domin ba su yarda da hadin kai a tsakanin musulmi ba.
Ayatullahi Karmani ya yi ishara da nasarar da aka samu akan kungiyoyin 'yan ta'adda tare da cewa hakan alkawali ne na Allah ne.