19 Nuwamba 2017 - 10:26
Shahadar Imam Ridha (AS)

A yau lahadi 30 ga watan Safar ne mabiya ahul Bait (a.s) Suke juyayin shahadar Imam Ridha, (a.s)

Imam Ridha wanda shi ne Imami na takwas a jerin Imaman ahlul baiti (a.s) ya yi shahada ne a ranar karshe ta watan Safar na shekarar hijira kamariyyah ta 203 a zamanin halifancin Ma'amun na daular Abbasiyya.

A kasashen da mabiya Ahlubaiti a.s suke suna raya dare da ranar shahadar Imam Ridha (a.s) da juyayi tare kuma da yin bayani akan rayuwarsa a cikin masallatai da kuma Husainiyoyi.