Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Bayt (a.s) – ABNA – ya bayar da rahoton cewa: jaridar Yahudawa ta "Ma'ariv," ta hanyar dogaro da rahoton tashar talabijin ta Kan, ta yi iƙirarin cewa ƙasashe da dama a yankin suna amfani da tattaunawa da Isra'ila a matsayin kayan aiki don rage matakin shirye-shiryen Tel Aviv, kuma a lokaci guda, a bayan fage suna shirye-shiryen wani babban rikicin soji akanta.
Bisa ga rahoton majiyoyin Isra'ila, cikakkun bayanai na wannan rahoto an buga su ne bayan makonni da yawa na hana bugawa kuma da izinin hukumar tantancewar sojin Isra'ila
Wannan rahoton ya yi iƙirarin cewa jami'an ɗaya daga cikin ƙasashen yankin sun shawarci jami'an wata ƙasa da su ci gaba da tattaunawa da Isra'ila da tsarin cimma yarjejeniya, amma manufar wannan yarjejeniya ba ita ce dogaro da ita na dogon lokaci ba; a'a, don haifar da jin kwanciyar hankali a Isra'ila da rage matakin tsaro na wannan tsarin, domin a ci gaba da shirye-shiryen soji a asirce.
Wannan rahoto ya kuma yi iƙirarin cewa a cikin waɗannan shawarwari, an ma ba da shawarar cewa a fara sanya hannu kan yarjejeniya da Isra'ila, sannan a keta ta a lokacin da ya dace. A da'awar Ma'ariv, wannan tsarin yana da kamanceceniya sosai da yanayin Yahya Sinwar kafin aikin 7 ga Oktoba; lokacin da Hamas a bayyane ke magana game da kwanciyar hankali, amma a lokaci guda tana shirye-shiryen kai hari.
Ma'ariv ta kara da cewa an fara buga wannan bayani ne a wani shirin labarai na talabijin na Isra'ila, kuma saboda takunkumin tantancewa, har yanzu ba a bayyana sunayen ƙasashen biyu da aka ambata ba.
Wannan jaridar a ƙarshe ta rubuta cewa damuwar hukumomin tsaro na Isra'ila ita ce, duk wata yarjejeniya ta siyasa a nan gaba, za ta iya zama kayan aiki don rage matakin shirye-shiryen wannan gwamnati, kuma dayan ɓangaren a wannan damar, ya samu kammala shirye-shiryensa na soji domin afkawa Isra'ilan.
.....................
Ra'ayinka