A ziyara ta sa a Nijer, Mista Zarif ya gana da mayan jami'an gwamnatin kasar da suka hada da firayi ministan kasar Birji Rafiji da kuma shugaba Isufu Mahamadu.
Babban jigon ziyarar dai shi ne karfafa alakar dake tsakanin kasashen biyu da tattauna batutuwan da suka shafi yankin da kuma na kasa da kasa.
A yayin ziyara ministocin harkokin waje na kasashen biyu sun jagoranci bude wani babban taron kasuwanci tsakanin Iran da Nijer.
Wannan ziyara ta Mista Zarif na zuwa ne bayan wacce ya kai a kasashen Afrika ta Kudu da kuma Uganda.288