21 Satumba 2017 - 17:45
 An Kashe 'Yan Ta'adda Fiye da 800 A Garin Dairzoor Na Syria

Sojojin kasar Rasha sun sanar da cewa jirgin yakinsu mai jefa bama-bamai ya kashe 'yan ta'adda 850 a jiya laraba

Kwamanda mai kula da yakin kasar syria na Sojojin Rasha, Sergei Rudskoi ya kara da cewa; A yayin harin, an kuma rusa tankokin yaki 11 da motoci masu sulke 46 da motocin akori-kura 20 da kuma wuraren ajiye makamai 38.

A cikin makwannin bayan nan, sojojin kasar ta Syria sun yi nasarar kwace yankuna masu yawa na Dairzoor daga hannun 'yan ta'addar.

Rasha ta shiga cikin yakin Kasar Syria ne tun a 2015 da zummmar taimakawa gwamnatin Basshar Assad a fadan da take yi da 'yan ta'adda.288