Tawagar shugabannin a karkashin Chief Edwin Clark ta ce sun ba Gwamnati bukatun 16 cikinsu har da yaki da talauci a Yankin domin kawo karshen hare haren da ake kai kan bututun mai, amma gwamnati ta kasa aiwatarwa.
A watan Nuwamban bara ne shugabannin yankin na Neja Delta suka mikawa shugaba Buhari bukatunsu 16, matakin da ya takaita hare haren tsagerun yankin akan kadarorin gwamnati.
Bukatun sun hada da dawo da dawo da manyan ofisoshin kamfanonin mai zuwa kudancin kasar da kara ware kudaden tallafi domin ci gaban yankin.
Mista Clarke ya ce za su fice tattaunawar idan har gwamnati ta gaza cimma bukatunsu.288