Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Bayt (AS) – ABNA – ya ruwaito cewa: Manjo Janar Wahidi, Babban Kwamandan Rundunar Kare Juyin Juya Hali a wani taron haɗin gwiwa da Manjo Janar Hatami, Babban Kwamandan Sojoji don nazarin halin da fagagen daga ya bayyana cewa: Ƙarfin soji na Sojojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya zarce tunanin maƙiya, a wannan yaƙi sun ga kuskuren lissafinsu game da ƙarfin sojojinmu a zahiri kuma gaskiyar soji ta Iran tana bayyanuwa a fagagen daga. Sojojin Isra’ila ba tare da tallafin Amurkawa ba za su ruguje cikin ɗan kankanin lokaci.
Babban Kwamandan Sojoji tare da nanata cewa haɗin kai da daidaiton da ke tsakanin Sojojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da Rundunar Kare Juyin Juya Halin Musulunci, ginshiƙi ne mai ƙarfi na tsaron ƙasa kuma makullin kaiwa ga kololuwar tsaro da ƙarfi ne inda ya bayyana cewa: haɗin kan da ba a iya raba shi tsakanin sojoji da rundunar kare juyin juya hali kamar yadda shugabannin juyin juya halin Musulunci suka yi tsammani kuma suka so, garkuwa ce ta ƙarfe da ke kare ƙasarmu daga fitinu, dabarun da kuma shirye-shiryen maƙiya.

Babban Kwamandan Rundunar Kare Juyin Juya Hali: Trump Ya Yi Kamun Kafa Da Ƙarya Da Yaudara Don Samun Nasarori
Manjo Janar Wahidi, Babban Kwamandan Rundunar Kare Juyin Juya Hali a taron haɗin gwiwa da Manjo Janar Hatami, Babban Kwamandan Sojoji:
Amurkawa sun ci karo da katangar imani da ƙwazon Iraniyawa kuma rashin ƙarfi da damuwa sun mamaye yanayi da shawarwarin Fadar White House.

Trump ya yi kamun kafa ga ƙarya da yaudara don samun nasarori. Hukumomin leƙen asiri da soji na Amurka da Sahayoniyawa, sun yaudari jami'an siyasa na Amurka game da ƙalubalen soji na Iran da juriyar Iran kuma a yau ma jami'an siyasa na Amurka suna yaudarar jama'ar Amurka don rufe kasawarsu.
………………
Ra'ayinka